Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan alummar Masar ya kai miliyan dari
2020-02-12 10:29:06        cri

Babbar hukumar fadakar da jama'a da kididdiga ta kasar Masar ta bayyana cewa, yawan al'ummar kasar ya kai miliyan 99. Hukumar ta bayyana cewa, adadin 'yan kasar dake gida ya kai miliyan 100, idan an kwatanta da miliyan 99 dake zaune a cikin kasar a ranar 22 ga watan Yulin shekarar da ta gabata, ban da baki 'yan kasar da yawansu ya haura miliyan 9.

Shugaban hukumar Khairat Barakat, shi ne ya shaidawa taron manema labarai a birnin Alkahiran na kasar Masar. Ya ce, matsalar yawan al'umma, ita ce babbar matsalar dake damun kasar, sannan babu ayyukan ci gaba ko na tattalin arziki da zai dore a cikin wannan yanayi da al'umma ke karuwa cikin sauri.

Gwamnatin kasar Masar ta bayyana damuwa cewa, wannan matsala ta yawan karuwar al'umma, za ta haifar da karin kalubale ga karancin albarkatu da jin dadin jama'a da tattalin arzikin kasar.

Wannan ne ya sa gwamnati, ta kaddamar da wani kamfel na shekaru biyu, mai taken "Biyu ya wadatar", da nufin rage karuwar yawan haihuwa. Haka kuma gwamnati, tana gina sabbin birane 20 na zamani, don inganta tsarin rayuwar jama'a, da fadada yankin gidajen kwana, ta yadda zai dace da karuwar yawan al'umma a kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China