Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin ya bada gudunmowa wajen ayyukan dogayen gine-gine a babban birnin Masar
2020-01-05 15:58:42        cri
Kamfananin gine-gine na kasar Sin wato (CSCEC), ya bayar da babbar gudunmawa wajen aikin zamanantar da kasar Masar ta hanyar gudanar da aikin gina wani bene mai hawa 20 a sabon yankin kasuwancin kasar mai tazarar kilomita 50 daga gabashin Alkahira, babban birnin kasar.

Babban jami'i mai kula da kamfanin na CSCEC dake Masar, ya bayyana cewa ginin sabon yankin hukumar gudanarwar babban birnin kasar da ake gudanarwa a halin yanzu, babban cigaba ne ga shirin bunkasuwa da kuma zamanantar da kasar Masar, ya ce aikin gina babbar cibiyar kasuwanci birnin wato (CBD), wanda kamfanin CSCEC ke gudanarwa yana da cikin muhimman ayyukan babban birnin kasar, in ji Chang Weicai, janar manajan CSCEC a Masar, ya bayyana a yayin zantawarsa ta kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Chang ya yi wannan tsokaci ne bayan wata liyafar da ya shirya wa firaiministan kasar Masar Mostafa Madbouly, da jakadan kasar Sin a Masar Liao Liqiang a yankin da ake gudanar da aikin dogon ginin mai hawa 20. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China