Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta tsawaita dokar ta baci da watanni 3
2020-01-15 10:17:57        cri
Majalisar dokokin kasar Masar, ta amince da tsawaita dokar ta baci dake akwai a kasar da watanni 3, saboda kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Mamban majalisar, Mohammed Abou Hamid, ya shaidawa Xinhua a jiya cewa, majalsiar ta amince da dokar shugaban kasar ta tsawaita dokar ta baci a kasar da karin wasu watanni 3, daga ranar 27 ga watan Junairu.

Karkashin dokar, sojoji da 'yan sanda za su dauki dukkan matakan da suka kamata, wajen tunkarar ta'addanci da tabbatar da tsaro a fadin kasar.

An sanya dokar ta baci a kasar ne karon farko, a watan Afrilun 2017, bayan hare-hare da aka kai wa wasu mujami'u 2, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane 47. Kuma tun daga wancan lokacin ake ci gaba da tsawaitawa.

Abou Hamid ya ce, tsawaita dokar za ta ba hukumomi masu ruwa da tsaki, amfani da damar da doka ta ba su na yaki da ta'addanci, yana mai cewa, daukacin mambobin majalisar ne suka kada kuri'ar amincewa da matakin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China