Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bukatar iskar gas ta karu a Afrika sakamakon bunkasuwar tattalin arziki
2020-01-14 09:25:44        cri
Ministan man fetur na kasar Masar ya ce bukatar da ake da shi ta iskar gas a Afrika ta ninka har sau biyu sakamakon kara samar da makamashi a cikin gida da bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar.

A jawabin da ya gabatar a taron dandalin kula da makamashin yankin Mediterranean, Tarek al-Molla ya ce, bukatar amfani da makamashin zai karu a duniya baki daya nan da shekaru 50 masu zuwa.

Amfani da iskar gas da man fetur da duniya ke yi a matsayin makamashi a halin yanzu ya kai kashi 80 bisa 100, ya kara da cewa, bukatar da ake da shi ta albarkatun iskar gas a matsayin makamashi zai cigaba da karuwa a duniya domin biyan bukatun daya bisa uku na al'ummar duniya nan da shekarar 2040.

Ministan ya jaddada muhimmancin da yankin Mediterranean ke da shi wajen samar da albarkatun iskar gas a kasuwannin kasa da kasa sakamakon gano karin sabbin yankuna masu makamashin ciki har da Masar.

Ya kara da cewa, amfani da albarkatun iskar gas shi ne kadai zabi game da tunkarar kalubalolin yaki da sauyin yanayi a yankin.

A bisa kididdigar shekarar 2019, kasar Masar tana samar da cubic mita biliyan 7.2 na albarkatun iskar gas a kullum. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China