![]() |
|
2020-02-07 13:09:39 cri |
Yayin tattaunawar ta su, Xi Jinping ya jaddada cewa, bayan bullar cutar numfashi a kasar Sin, gwamnati da al'ummar kasar, dukkansu sun dukufa wajen yaki da cutar. Ya ce, "Mun yi kira ga dukkanin al'ummomin kasar Sin, su shimfida ayyukan yaki da cutar bisa dukkan fannoni, da aiwatar da ayyukan cikin sauri, da kuma daukar matakai masu tsanani, domin yin kandagarki, da hana yaduwar cutar numfashi a kasar Sin."
Ya ce, "A yanzu haka, mun cimma wasu nasarori, kuma Sin tana da imanin cimma nasarar wannan yaki. Kana, matsalar ba za ta hana bunkasuwar tattalin arzikin kasar a nan gaba ba." (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China