![]() |
|
2020-02-07 11:24:03 cri |
Yayin zantawar tasu a jiya Alhamis, shugaba Xi ya nuna matukar godiyarsa ga yariman, da masarautar saudiyya, bisa goyon bayan da suke nunawa Sin musamman ma a wannan lokaci da kasar ke yaki da annobar coronavirus.
Shugaban na Sin ya ce kasarsa, na dora muhimmancin gaske ga harkar kiwon lafiyar daukacin al'ummun kasashen waje dake zaune a cikin kasar, ciki hadda Saudiyya, za ta kuma ci gaba da daukar kwararan matakai, na kyautata zaman rayuwar su a wuraren da suke zaune.
A nasa bangare, Yarima Salman ya mika sakon goyon bayan masarautarsa ga kasar Sin, yayin da ake tsaka da yaki da wannan annoba, yana mai taya al'ummar Sin alhinin barkewar wannan cuta, wadda ta hallaka mutane da dama. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China