Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi shirin yiwa dokar kiyaye dabobbin daji gyaran fuska
2020-02-11 10:26:17        cri
Direktan ofishin kula da dokar tattalin arziki na kwamitin doka da shari'a na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wang Ruihe ya bayyana a jiya Litinin cewa, kwamitin ya riga ya fara aikin yiwa dokar kiyaye dabobbin daji gyaran fuska, inda ake shirin shigar da wadannan gyare-gyare cikin aikin kafa doka da kwamitin zai gudanar a bana, da ingiza aikin yiwa dokar yin kandagarki dake da nasaba da dabobbi gyaran fuska.

Bayanai na cewa, dokar dake shafar dabobbin daji kai tsaye a kasar Sin a halin yanzu ita ce dokar kiyaye dabobbi. A shekarar 2016 aka yiwa dokar gyaran fuska don magance matsalar cinye dabobbin daji yadda ake so, baya ga kafa wani tsari na zamani, amma duk da haka ba a kaucewa fuskantar wasu matsaloli ba, a cewar Wang Ruihe, alal misali, ba a sanya ido da gudanar da wannan doka yadda ya kamata, haka kuma ba a kawar da wasu kasuwannin sayar da naman daji, shi ya sa a wasu wurare kasuwar sayar da naman daji ta bunkasa matuka, abin da ya kawo babbar illa ga lafiyar jama'a. Don haka ya jaddada cewa, ya kamata a yiwa wannan doka gyaran fuska don kara karfin daidaita wannan matsala daga tushe. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China