Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na kara azama kan yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar daidaita sauyin yanayi
2019-10-17 11:10:27        cri

Jiya Laraba mataimakin ministan harkokin muhalli na kasar Sin Zhuang Guotai, ya bayyana a birnin Changsha cewa, kasar Sin na himmantuwa wajen kara azama kan yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar daidaita matsalolin sauyin yanayi.

A yayin taron dandalin tattaunawa kan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba na nahiyar Asiya da tekun Pasifik na shekarar 2019, Zhuang Guotai ya ce, tun bayan shekarar 2011, kasar Sin ta ware kudin Sin RMB fiye da biliyan 1 baki daya wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar daidaita sauyin yanayi, a kokarin marawa sauran kasashe masu tasowa baya gwargwadon karfinta, da kuma more kyawawan fasahohin daidaita sauyin yanayi da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.

Haka zalika, ya zuwa yanzu, kasar Sin, kasa mai tasowa ce mafi girma a duniya. Za ta tsaya kan bin ka'idojin "sauke nauyin bai daya amma akwai bambanci", da yin adalci kuma gwargwadon karfin daidaikun kasashe. Za ta kuma aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, a kokarin hada kai da sassa daban daban wajen neman samun kyakkyawar makoma a nan gaba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China