Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na kokarin samar da makamashin lantarki ta hanyoyin da ba sa gurbata muhalli
2019-12-11 11:01:01        cri
Wasu alkaluman kididdigar tattalin arzikin kasar Sin karo na hudu ya nuna cewa, kasar ta samu gagarumin cigaba wajen samar da makamashin lantarki ta hanyoyin da bas a gurbata muhalli tsakanin shekarun 2014-2018, yayin da kasar ke cigaba da fadada hanyoyin samar da makamashi mai tsabta a fadin kasar baki daya.

A shekarar 2018, kasar ta samar da karfin lantarki da ya kai kilowatt tiriliyan 7.1 a cikin sa'a guda, wanda ya karu da sama da kashi 31.3 bisa 100 a shekarar 2013, kamar yadda rahoton kididdigar tattalin arzikin kasar wanda hukumar kididdiga ta kasar NBS ta fitar a ranar Litinin.

Adadin yawan wutar lantarkin da aka samar a shiyyar yammacin kasar Sin ya dara na dukkan shiyyoyin kasar a cikin shekaru biyar, inda yake samun karuwar kashi 42.3 bisa 100 tun daga shekarar 2013, rahoton ya yabawa shirin samar da makamashi mai tsabta da bangaren gina tashoshin samar da lantarkin kasar.

A bisa kididdigar, makamashin da ake konawa don samar da wutar lantarki daga tururi ya karu da kashi 20 bisa 100 daga shekarar 2013 zuwa kilowatt tiriliyan 5.1 a sa'a guda, wanda ya yi kasa da kashi 71.8 bisa 100 na karuwar makamashi mai tsabta. Adadin samar da wutar lantarki daga tururi ya ragu da kashi 6.7, wanda ya kai kashi 71.5 na dukkan makamashi mai tsabta da ake samarwa a fadin kasar ta Sin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China