Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban gandun dajin kasar Sin mai dausayi dake kudancin tsibirin Hainan ya karu sosai
2019-09-02 10:40:23        cri

Rahotanni daga kasar Sin na cewa, gandun dajin kasar mai dausayi mafi girma dake kudancin tsibirin Hainan, ya karu da kimanin eka 200,000 a cikin shekaru ashirin da suka gabata. An samu wannan ci gaba ne biyo bayan matakan wayar da kan jama'a game da kariya da yaki da talauci da gwamnatin kasar Sin ta bullo da su, da nufin hana mazauna yankin su sare itatuwa da kona daji don yin farauta.

Hukumar kula da gandun daji ta lardin Hainan, ta bayyana cewa, a shekarar 2018 da ta gabata, girman yankin gandun daji mai dausayi na lardin ya kai eka 659,300, kana fadin yankin da aka kare ya karu daga kasa da kaso 90 cikin 100 zuwa kaso 98.16 cikin 100 a cikin shekaru ashirin din da suka gabata.

Gandun daji mai dausayi dake Hainan, shi ne mafi girma a duk fadin kasar Sin, wanda ke kunshe da nau'o'in halittu da dama da wadanda ke kokarin bacewa daga doron kasa.

A shekarun 1990, lardin Hainan ya haramta sare itatuwa a baki dayan gandun dajin, inda aka bullo da matakan dasa itatuwa wadanda suka taimaka wajen farfado da gandun daji na ainihi.

Jami'an na bayyana cewa, shirin yaki da talauci ya taimaka wa yadda aka kare gandun daji mai dausayi, matakin da ya samar da kudin shiga ga manoma da kare muhalli da kiwon zuma a yankuna masu fama da talauci don maye gurbin yadda aka sare itatuwa da yin farautar dabbobi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China