Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kaddamar da asusun raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba a shekarar 2020
2019-12-26 20:26:28        cri
Ma'aikatar kare muhalli da halittu ta kasar Sin, ta bayyana cewa, a shekarar 2020 kasar za ta kaddamar da asusun raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, a wani mataki na inganta manufofin tattalin arziki da ke shafar kare muhalli da muhallin halittu.

Jami'in ma'aikatar Xu Bijiu ya shaidawa taron manema labarai a birnin Beijing cewa, wadannan manufofi, za su karfafawa kamfanonin cikin gida gwiwar rage fitar da hayakin dake gurbata muhalli, kuma sun kasance muhimmin mataki na magance matsalolin dake shafar muhalli.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China