Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da shirin dakile amfani da robobi masu gurbata muhalli nan da shekarar 2025
2020-01-20 10:01:14        cri
Mahukuntan kasar Sin sun fitar da wani shiri, na dakile amfani da nau'oin roba mai gurbata muhalli nan da shekarar 2025. Manufar shirin dai ita ce rage kaso mafi yawa, na nau'in roba da leda dake lalata muhalli, za kuma a aiwatar da shirin cikin shekaru 5.

Wani kundin bayani da hukumar tsara ayyukan ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar ta fitar, ya nuna cewa matakan da za a aiwatar, sun hada da na hana samar da wasu nau'oi na leda, da hana sayar da su, da kuma yayata amfani da wasu nau'oin ledar dake iya rubewa a kasa, ko wadanda ake iya sabunta amfani da su.

Kundin ya nuna cewa, nan da shekarar 2025, Sin na fatan shawo kan matsalar yaduwar robobi masu lalata muhalli, da rage kaso mai yawa na bolar ledoji dake cika sassan biranen kasar, da kuma kafa tsarin kula da nau'oin roba da ake amfani da su a kasar, tare da samar da madadin wadanda aka haramta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China