Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin jihar Lagos ta Najeriya ta dauki matakin tinkarar cutar Corona da Lassa
2020-02-11 10:11:17        cri
Jaridar Vanguard ta Najeriya ta ba da labari cewa, babban jami'in hukumar kula da aikin kai agajin gaggawa ta kasar wato LASEMA, Olufemi Oke-Osanyitolu ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Lagos ta kafa wani kwamiti mai mutane 5 karkashin wannan hukuma, don daukar matakan yaki da cutar numfashi ta corona da Lassa wato shirin EPRP. Sa'i daya kuma, gwamnatin tana sintiri a kasuwannin sayar da dabbobi da naman daji dake cikin jihar. Olufemi ya jaddada cewa, ya zuwa yanzu, babu wanda ya kamu da cutar corona a jihar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China