Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar mabiya addinin Kirista ta Nijeriya ta bukaci gwamnatin kasar ta yi amfani da fasahar zamani wajen yaki da rikice-rikice
2020-02-08 16:41:38        cri

Kungiyar mabiya addinin Kirista ta Nijeriya (CAN), ta yi kira ga gwamnatin kasar, ta yi amfani da tsarin fasaha ta zamani wajen shawo kan matsalolin tsaro.

Shugaban kungiyar CAN, Samson Ayokunle ya bayyana a jiya cewa, a wannan zamanin da ake ciki, inda ake kafa nau'rorin kyamara na sa ido a ko ina, bai kamata masu aikata laifi su rika yawo ba tare da an kama su ba, inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta kama bata garin dake aikata laifuka da kashe-kashen mazauna kasar.

A ranar Litinin da ta gabata ne shugaban majalisar dattawan kasar, Ahmad Lawan, ya ce Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, da shugabannin majalisar dokokin kasar, sun bayyana damuwa matuka dangane da kalubalen tsaro da ake fama da shi a kasar, ciki har da sace sacen mutane da fashi da makami, inda suka amince da yin dukkan mai yuwuwa wajen magancesu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China