Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar Nijeriya ta yi kira da a koyi fasahohin Sin na kandagarkin yaduwar cututtuka
2020-02-07 10:07:16        cri
A ranar 5 ga wata, jaridar Leadership ta Nijeriya ta fidda wani sharhi, inda a cikin sa ta nuna yabo kan yadda kasar Sin take dukufa wajen hana yaduwar cutar numfashi, inda sharhin ya kuma yi kira ga gwamnatin kasar da ta yi koyi daga kasar Sin wajen hana yaduwar cututtuka a Najeriya, kaman cutar Lassa da dai sauransu.

 

Sharhin ya ce, bayan barkewar cutar ba zato ba tsammani, gwamnatin kasar Sin ta gano asalin cutar cikin sauri, sa'an nan, ta yi kira ga dukkanin al'ummomin kasar, da su dauki matakai bisa dukkan fannoni, ciki har da samar da kudaden kandagarkin yaduwar cutar cikin gaggawa, da tura masu aikin likitanci na wurare daban daban zuwa birnin Wuhan, da kafa asibitocin musamman, dake da gadaje sama da dubu 2, da kuma gabatar da bayanai ba tare da boye komai ba, da yin hadin gwiwa da kasa da kasa, da dai sauransu.

Hakan a cewar sharhin ya wuce bukatun "ka'idar kiwon lafiyar kasa da kasa". Haka kuma, cikin sharhin, jaridar Leadership ta nuna cikakken goyon bayan ta ga gwamnati da al'ummomin kasar Sin.

Bugu da kari, ta ce, idan aka kwatanta da yadda kasar Sin take yaki da cutar numfashi a yanzu, ana iya cewa, aikin da gwamnatin Nijeriya ta yi domin fuskantar matsalar cutar Lassa ba shi da karfi sosai. Don haka ya kamata gwamnatin kasar ta yi koyi da kasar Sin, ta samar da kudaden da ake bukata, da kuma gaggauwa wajen kawar da cutar Lassa a duk fadin Nijeriya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China