Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kaddamar da hari kan maboyar 'yan Boko Haram
2020-02-06 11:18:29        cri
Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta sanar a jiya Laraba cewa wata rundunar tsaron sojojin ta musamman ta kaddamar da hare hare don tarwatsa wasu wuraren fakewar 'yan ta'adda a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar da kakakin rundunar sojojin saman kasar ta NAF, Ibikunle Daramola, ya ce, sun fara kaddamar da aikin sintirin ne a ranar Talata, inda suka zabi wasu yankuna a shiyyar arewa maso gabashin kasar domin tarwatsa maboyar 'yan ta'adda da nufin hana su samun sukuni.

Hare haren ta jiragen sama da NAF suka kaddamar a ranar Talata ya yi nasarar lalata mafakar mayakan 'yan ta'adda na IS dake yammacin Afrika da kuma kashe mayakan kungiyar da dama a yankin Tongule, dake bangaren tafkin Chadi a arewacin jihar Borno, inji jami'in.

Daramola ya ce, hukumar NAF, tana da cikakken karfin kaddamar da hare haren ta sama, a kokarin da take na ayyukan murkushe mayakan 'yan ta'adda a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China