Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sandan Nijeriya sun kashe tsageru 250 yayin wani samame
2020-02-07 11:05:13        cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta ce jami'anta sun kashe tsagerun kungiyar masu tsattsauran ra'ayi, da addainsu ya kai 250, yayin wani samame da suka kai jihar Kaduna dake arewa maso tsakiyar kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Frank Mba ya fitar, ta ce daga cikin wadanda aka kashe, akwai shugabannin kungiyar Ansaru. A ranar Laraba ne 'yan sanda, bisa rakiyar jirage masu saukar ungulu, suka kai samame mobayar kungiyar dake dajin Kuduru na jihar Kaduna.

A cewarsa, samamen da aka kai dajin Kuduru dake makwabtaka da yankin Birnin Gwari, ya shafe sa'o'i da dama.

Frank Mba ya kara da cewa, kungiyar Ansaru ta dade tana addabar yankin arewacin kasar, inda take kashewa tare da sace mutane, da kuma aikata wasu laifuffuka.

A cewar wata kafar yada labarai ta kasar, kungiyar Ansaru ta sanar da kafuwarta ne a shekarar 2012, kuma tun daga lokacin take sace-sacen mutane, musammam 'yan kasashen waje. Rahotanni na cewa, kungiyar wani tsagi ne na kungiyar Boko Haram. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China