Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya sha alwashin samar da kayayyakin aiki ga sojoji
2020-02-07 11:16:16        cri
Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi alkawarin samar da karin kayayyakin yaki na zamani ga rundunar sojojin kasar, a gabar da dakarun ke dauki ba dadi da 'yan ta'adda a wasu sassan kasar.

Shugaban Najeriyar ya yi wannan alkawari ne a jiya Alhamis, lokacin da ya kaddamar da jirage masu saukar ungulu kirar Agusta 109 biyu, da kuma Mi-17 E guda daya, wadanda kasar ta sayo domin ayyukan tsaro, yayin bikin da ya gudana a birnin Abuja fadar mulkin kasar.

Shugaba Buhari ya ce za a kara inganta kwarewar aiki ta jami'an tsaro, za kuma a samar da kayan aiki na zamani, wadanda za su dace da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, yana mai alkawartawa 'yan kasar ganin bayan ayyukan 'yan ta'adda, da suka zame wa kasar kadangaren bakin tulu.

Shugaban ya kuma yi kira ga sojojin saman kasar, da su rika aiwatar da ayyukan su bisa doka, su kuma kiyaye kayan aikin su yadda ya kamata, ta yadda kasar za ta ci gajiyar su a tsawon lokaci. Ya ce jiragen da aka samar za su taimaka, wajen kaddamar da hare hare ta sama, kamar dai yadda bukatar hakan ta bayyana a fannin tsaron kasar.

Daga nan sai ya jinjinawa dakarun soji, da sauran jami'an tsaron kasar, yana mai kira da a samar da karin hadin kai na daukacin sassan tsaron, domin ganin bayan kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China