Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda kasashen Afirka suka nuna goyon baya ga kasar Sin a kokarinta na yaki da cutar coronavirus ya shaida zumuncin dake tsakaninsu
2020-02-10 19:23:28        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang, a yau Litinin ya bayyana cewa, a daidai lokacin da ake kokarin dakile cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa, kasashen Afirka sun baiwa kasar Sin tsayayyen goyon baya, matakin da ya shaida sahihin zumunci dake tsakaninsu.

A gun taron manema labarai da aka shirya ta yanar gizo, Mr. Geng Shuang ya ce, taron ministocin kungiyar tarayyar Afirka da ya gudana a kwanan baya, ya bayar da sanarwar musamman, inda gaba daya ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar suka sanar da cewa, suna tare da gwamnatin kasar Sin da ma al'ummarta, kuma suna goyon bayan kasar Sin kan kokarin da take yi na dakile cutar. Baya ga haka, sun kuma yi kira ga kasa da kasa, da su hada kawunansu da kasar Sin, don tinkarar cutar.

Kakakin ya kara da cewa, kungiyar 'yan Habasha dake dalibta a birnin Wuhan, ta fitar da takardar nuna goyon baya ga kasar Sin, da kuma birnin Wuhan. Kazalika wasu 'yan kasashen Afirka da ke dalibta a kasar Sin sun bukaci a ba su aikin sa kai a sassan ba da jinya, ko kuma tashoshin jiragen kasa. Bayan da aka kawo karshen cutar, zumuncin dake tsakanin al'ummomin Sin da Afirka zai kara karfafa, kuma makomar bai daya za ta kara tabbata gare su. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China