Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar lafiya ta kasar Sin ta ce ana samun karuwar masu warkewa daga cutar numfashi
2020-02-10 20:15:13        cri
Kakakin hukumar lafiya ta kasar Sin Mi Feng, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka tattara, sun nuna yadda ake samun karuwar yawan masu warkewa daga cutar numfashi ta coronavirus, a sassan kasar Sin daban daban.

Mi Feng ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, karkashin shirin hadaka na majalissar gudanarwar kasar, wanda aka dorawa alhakin lura da aikin tabbatar da kandagarki, da kuma shawo kan cutar.

Mi Feng, ya ce a baya bayan nan, alkaluman warkewar masu fama da cutar a fadin kasar, sun kai kaso 8.2 bisa dari, sama da kaso 1.3 bisa dari da aka samu a ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata. A lardin Hubei kadai, alkaluman wadanda suka warke a wannan gaba ya kai kaso 6.1 bisa dari, wanda ya haura kaso 1.7 bisa dari da aka samu a ran 27 ga watan Janairu.

Ya ce a birnin Wuhan kadai, adadin ya kai kaso 6.2 bisa dari, sama da kaso 2.6 bisa dari da aka samu a ranar 27 ga watan Janairu. Bugu da kari, fadada sassan ayyukan jinya ta hanyar samar da karin jami'ai, da samar da karin gadajen kwantar da marasa lafiya a lardin Hubei da birnin Wuhan, sun taimaka matuka wajen samar da karin nasarori. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China