![]() |
|
2020-02-10 16:32:42 cri |
A kwanakin baya, manyan jami'an kasashe da dama na duniya sun buga waya ga ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, inda suka nuna goyon baya da yabo ga kasar Sin domin ta dauki matakai masu amfani wajen yaki da cutar coronavirus. Amma akwai wasu bangarori da suka nuna shakka ga kasar Sin wajen hana yaduwar cutar a sauran kasashen duniya.
Game da wannan batu, Geng Shuang ya bayyana a gun taron manema labaru ta yanar gizo cewa, cutar coronavirus kalubale ne da dan Adam ke fuskanta tare, ana bukatar kasa da kasa da su tinkari yaki da cutar tare.
Geng Shuang ya yi nuni da cewa, a halin yanzu Sin tana gudanar da ayyukan yaki da cutar yadda ya kamata, an samu babban ci gaba, yawan mutanen da suka warke daga cutar sun zarce yawan wadanda suka mutu a sakamakon cutar, kana adadin yawan sabbin mutanen da ake zaton sun kamu da cutar yana raguwa matuka. Sin tana da imani da karfi wajen cimma nasarar yaki da cutar coronavirus, da yin kokari tare da kasa da kasa wajen tabbatar da kiwon lafiya a cikin kasar har ma da dukkan duniya baki daya. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China