Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahukuntan kasar Sin sun jaddada bukatar samar da muhimman kayayyakin lafiya doin yaki da annobar Corona
2020-02-11 09:27:48        cri
Hukumomin kasar Sin sun kara jaddada bukatar samarwa da wadatar da muhimman kayayyakin kandagarki da hana yaduwa, da tura ma'aikatan lafiya da magungunan yaki da cutar numfashi da ta bulla a kasar.

Taron babban kwamitin yaki da cutar annobar Corona na kwamitin tsakiya na JKS, wanda Firaministan kasar Sin kana mamban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na JKS Li Keqiang ya jagoranta, ya ce , ya kamata a dauki matakan da suka dace wajen karba da ma kula da marasa lafiyan da suka kamu da kwayar cutar da rage kamuwa gami ga mace-mace.

Bugu da kari, taron ya umarci kananan hukumomi da su karfafawa kamfanoni gwiwar kara samar da kayayyakin kiwon lafiya, kamar rigunan kariya da abin rufe baki da fuska, ta hanyar samar da dabaru, da tsarin haraji da manufofin kudi da manufofin sayen kayayyaki da adana su ga gwamnati da taimakawa wajen rage matsalar karancin muhimman kayayyaki da 'yan kwadago.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China