Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD da AU sun ci gaba da nuna goyon baya ga Sin wajen yaki da cutar coronavirus
2020-02-10 13:01:40        cri

Shugabannin kungiyar AU da jami'an MDD da sauran mahalarta taron kolin kungiyar AU karo na 33 dake gudana a birnin Addis Abba na kasar Habasha sun nuna goyon baya ga kasar Sin wajen yaki da cutar coronavirus.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres dake halartar taron ya bayyana a ranar 8 ga wata cewa, Sin ta yi namijin kokari wajen yaki da cutar, don haka ya kamata kasashen duniya su hada kai don ganin bayan wannan cuta. Kana ya yi kashedi cewa, bai kamata bangarori daban daban su rika zargin kasar Sin domin wannan cuta ba.

Shugaban babbantaron MDD karo na 74 Tijjani Muhammad-Bande ya bayyana yayin da yake halartar taron a ranar 8 ga wata cewa, ya kamata a kara yin hadin gwiwa da daina yada jita-jita yayin da ake yin kokarin yaki da cutar.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat ya bayyana a gun taron shugabannin kungiyar AU da aka bude a jiya cewa, a wannan lokaci, mun ji yadda abokanmu Sinawa suke ji wajen yaki da cutar coronavirus. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China