Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kashi 70 cikin dari na kamfanonin Sin masu samar da abinrufebaki da hanci sun fara aiki
2020-02-10 10:57:40        cri

Bayan da cutar coronavirus ta bulla a kasar Sin, jama'ar kasar sun kara bukatar samar da kayayyakin rayuwar yau da kullum. Game da wannan batu, majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayar da sanarwa game da tsarin tinkarar cutar coronavirus, inda ta bukaci kamfanonin kasar su dawo aiki bayan hutun bikin bazara.

Bisa labarin da kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya bayar, ya zuwa ranar 7 ga wannan wata, yawan kamfanonin samar da abin rufe baki da hanci da suka fara aiki a kasar ya kai kashi 73 cikin dari. Yawan kamfanonin samar da hantsi, da kayayyaki da suka dawo bakin aikinsu a kasar ya kai kashi 94.6 cikin dari. Yanzu ana samar da iskar gas, da wutar lantarki, da man fetur, da kuma jigilar jiragen sama, da na kasa, da na ruwa yadda yakamata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China