2020-01-22 09:40:46 cri |
Lamarin wanda ya faru a Juma'ar da ta gabata ya haifarwa Maiduguri, babban birnin jahar Borno, katsewar hasken wutar lantarki, kamar yadda wata sanarwa daga kamfanin rarraba wutar lantarki ta Najeriya (TCN) ya fitar.
TCN, wanda shi ne ke da alhakin rarraba wutar lantarki a kasar, ya ce wasu mayakan Boko Haram sun lalata kayayyakin samar da lantarki a Maiduguri a lokacin da suka kaddamar da harin. Harin ya kuma yi sanadiyyar lalata wutar lantarkin a garin Damaturu, birnin dake makwabtaka da jahar Borno a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
A watan Yunin shekarar 2019, kamfanin samar da lantarki dake yankin ya zargi kungiyar Boko Haram da lalata na'urorin wutar lantarki a garin Molai, dake Maiduguri, lokacin da suka kaddamar da hari a yankin. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China