Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe shaguna 199 dake sayar da gas ba bisa ka'ida ba a Nijeriya
2020-01-24 14:37:27        cri
An rufe shaguna akalla 119 masu sayar da gas ba bisa ka'ida ba a Kaduna dake arewacin Nigeria, biyo bayan fashewar kurtun gas a farkon watan nan, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka.

Shugaban hukumar kula da muhalli na jihar Kaduna, Jibrin Lawal, ya ce rufe shagunan ya biyo bayan umarnin da gwamnan jihar ya bayar, bayan an samu fashewar kurtun gas a ranar 4 ga wata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 8, yayin da wasu 4 suka jikkata.

A ranar 7 ga wata ne gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar, ya bada umarnin rufe duk wani shagon dake sayar da gas ba bisa ka'ida ba, dake da mazauni a unguwannin jama'a a fadin jihar.

Umarnin ya zo ne kwanaki 3 bayan aukuwar gobarar a wani shago dake unguwar Sabon Tasha, ta yankin karamar hukumar Chikun.

Jibrin Lawal ya kara da cewa, aikin cika kurtun gas na da hadari sosai da bai kamata a yi shi a yankunan unguwannin jama'a ba.

A cewarsa, jimillar shagunan cika gas masu lasisi 77 ne aka rufe har zuwa lokacin da suka tabbatar da daukar matakan kariya, yayin da aka rufe guda 42 da ba su da lasisi, a wani mataki na kare aukuwar hadari. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China