Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnonin Najeriya na daukar matakan dakile cutar zazzabin Lassa
2020-01-24 14:29:41        cri
Gwamnoni a tarayyar Najeriya, suna hada kai da hukumomin lafiya a kasar, ta yadda za a kara zage damtse a kokarin da ake na dakile cutar zazzabin Lassa a kasar.

Shugaban kungiyar gwamnonin kasar (NGF) Kayode Fayemi, shi ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar, yana mai cewa, kungiyar ta samu karin bayani game da cutar.

Ya ce, ya yi imanin cewa, gwamnatocin jihohin kasar tare da hadin gwiwar ma'aikatar lafiya ta tarayya da cibiyar yaki da cututtuka ta kasa (NCDC), suna dakar matakan riga kafi don ganin cutar ba ta kara yaduwa ba.

A farkon wannan shekarar ce dai, aka ba da rahoton bullar cutar a wasu sassn kasar ta Najeriya. Ya zuwa yanzu dai a kalla mutane 19 da suka hada da wata mata mai juna biyu da ma'aikatan lafiya biyu ne cutar zazzabin Lassa da ta barke a Najeriyar ta halaka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China