Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta mika sakon ta'aziyyar rasuwar Robert Mugabe
2019-09-06 19:11:08        cri

Mahukuntan kasar Sin, sun gabatar da sakon ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe. Da yake tabbatar da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Geng Shuang, ya bayyana tsohon shugaban da dattijon arziki, wanda ya yi tsayin daka wajen 'yantar da kasar sa.

Geng Shuang ya ce Mugabe ya yi rayuwa mai cike da kokarin kare martabar kasarsa, da ikonta na cin gashin kai, ya kuma yi duk mai yiwuwa, wajen dakile tsoma bakin sassan waje cikin al'amuran Zimbabwe.

Ya ce Mugabe ya yi rawar gani wajen bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasarsa, da ma irin kawancen dake tsakanin Sin da sauran kasashen Afirka baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China