Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Matakin wasu kasashe na katse zirga-zirgar sama da Sin ba shi da amfani ga hana yaduwar cutar numfashi
2020-02-06 16:46:34        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana a nan birnin Beijing a yau cewa, wasu kasashe sun dauki mataki mai tsanani, na katse zirga-zirgar sama da kasar Sin. A cewar ta, hakan ba zai yi wani amfani a fannin hana yaduwa, ko kandagarkin cutar ba. A maimakon haka zai haifar da tsoro, kuma zai kawo cikas ga tuntubar jama'ar kasa da kasa, da ma hadin kan kasa da kasa, har ma zai kai illa ga odar zirga-zirgar sama ta kasashe daban-daban. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China