Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta samu gagarumar nasara wajen hana yaduwar cutar AIDS
2019-12-02 10:28:27        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin (NHC) ta bayyana cewa, kasar ta samu nasara wajen hana yaduwar cutar kanjamau (AIDS) inda adadin yaduwar cutar ya yi kasa matuka. Hukumar ta bayyana a shafinta na WeChat cewa, an yi nasarar dakile yadda ake yada cutar ta hanyar ba da jini, sa'an nan an hana yaduwar cutar ta hanyar yin allurar miyagun kwayoyi da ma yadda uwa take yada cutar ga jaririn dake cikinta.

A cewar hukumar, ya zuwa karshen watan Oktoban wannan shekara, akwai mutane 958,000 dake dauke da kwayar cutar a kasar Sin, bayan rahoton da ke nuna cewa, akwai sabbin mutane 131,000 da suka kamu da cutar a watanni 10 na farkon wannan shekara.

Hukumar ta NHC ta tsara matakan da suka dace na hana yaduwar cutar ta hanyar jima'i, babbar hanyar da a halin yanzu ake yada cutar a kasar Sin da magance yadda mahaifiya ke yada cutar ga jaririn da ke cikinta.

Yanzu haka hukumar ta ce, an gano lardunan da cutar ta fi kamari da yankunan dake fama da talauci da ma matasa baligai da dalibai, a matsayin aiki mai muhimmanci na kawar da wannan cuta.

Hukumar ta lashi takwabin karfafa matakai na ilimantar da jama'a game da nauyin dake wuyansu a bangaren kiwon lafiya da hukunta masu keta doka da manyan laifukan da suke da nasaba da yada cutar AIDS, da matakan kariya gami da magance cutar da makamantansu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China