Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da asibitin Leishenshan a birnin Wuhan yau
2020-02-05 17:20:21        cri

Yau Laraba 5 ga watan Fabrairu an kaddamar da sabon asibitin Leishenshan da aka gina a birnin Wuhan, inda za'a gudanar da aikin jinyar mutanen da suka kamu da annobar sabuwar kwayar cutar numfashi ta coronavirus, kawo yanzu an kammala aikin ginin asibitin. Kafin wannan lokacin an kaddamar da asibitin farko na Huoshenshan wanda aka kammala ginawa a birnin, inda aka fara kwantar da marasa lafiya a ranar Talata 4 ga watan Fabrairu.

Sabon asibitin na Leishenshan, an fara gina shi a ranar 26 ga watan Janairu, yana da fadin murabbi'in mita 79,700, yana dauke da gadaje 1,600 kuma zai iya daukar ma'aikatan jiyya sama da 2,000.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China