Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na shirin sanya dokar takaita shan sigarin lantarki
2019-07-23 11:06:18        cri

Hukumar kula da lafiya ta kasar Sin NHC, na shirin takaita shan sigarin lantarki ta hanyar sanya doka, domin magance damuwar da ake da ita kan illolin sigarin.

Shugaban sashen shirye-shirye na hukumar NHC Mao Qunan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, a yanzu, hukumar na gudanar da bincike da hadin gwiwar sassa masu ruwa da tsaki game da batun.

Mao Qunan ya ce, bayanai sun nuna cewa, sinadarin aerosol da irin sigarin ke samarwa na da wasu sinadarai masu guba, kuma abubuwan dake cikinsa na barazana ga lafiyar masu shansa.

A cewar wani nazari da hukumar takaitawa da kare cuttutuka ta kasar Sin ta yi a bara, duk da Sinawa masu shan sigarin ba su da yawa, adadinsu ya rubanya a shekarar 2015.

Nazarin ya ce adadin ya fi yawa a tsakanin matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 24, fiye da sauran rukunin shekaru.

Mao Qunan, ya ce la'akari da barazanarsa da kuma mummunan tasirinsa kan halayyar matasa, ya kamata a takaita shan sigarin sosai. Yana mai cewa ya kamata a kara wayar da kan al'umma game da illolin sigarin na lantarki, musammam iyaye da makarantu domin kare matasa daga shansa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China