Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu amfani da yanar gizo na Sin suna sa lura game da gina asibitocin wucin gadi a Wuhan
2020-02-06 10:04:38        cri

A halin yanzu, ana kokarin gina asibitocin wucin gadi ta hanyar gyara zauren motsa jiki, da filin nune-nune, don kwantar da wadanda suka kamu da cutar numfashi, suke kuma cikin yanayi maras tsanani.

Manhajar gabatar da bidiyo ta babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya gabatar da bidiyon gina asibitocin wucin gadi kai tsaye. Ya zuwa daren ranar 5 ga wannan wata, mutane fiye da miliyan 100 sun kalli wannan bidiyo, wanda ake kiran su da masu sa ido ta yanar gizo.

A ranar 3 ga wannan wata ne aka fara gina asibitocin wucin gadi a birnin Wuhan, don kwantar da wadanda suka kamu da cutar numfashi, suke kuma cikin yanayi maras tsanani. A halin yanzu, ana kokarin gina asibitocin wucin gadi guda 13, wadanda yawan gadajen dake cikin su zai kai fiye da dubu 10.

An rika wallafa bidiyon gina asibitocin kai tsaye dare da rana. Kafin wannan, an gabatar da bidiyo game da gina asibitin Huoshenshan, da na Leishenshan kai tsaye, a manhajar gabatar da bidiyo ta CMG, wanda ya jawo hankalin masu amfani da yanar gizo miliyan 90, wadanda suka kalli aikin gina asibitocin a kan internet. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China