Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Amurka za ta martaba kokarinta wajen dakile annobar cutar numfashi
2020-02-04 12:12:16        cri
Game da tsokacin da wasu Amurkawa suka yi kan annobar numfashin da take bazuwa a kasar Sin, yau Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying ta bayyana cewa, ya dace Amurka ta martaba kokarin da kasar Sin take yi domin dakile bazuwar annobar, haka kuma ta dauki matakai bisa adalci, da hankali tare da sauran kasashen duniya, ta yadda za a kawo karshen yaduwar annobar cikin lokaci.

Kana kasar Sin ta lura cewa, sau tari, Amurka na bayyana cewa, za ta samar da tallafi ga kasar Sin, a don haka, tana sa ran Amurka za ta gabatar da taimakon na ta da wuri. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China