Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AMISOM ta yi kira da a kawo karshen muzgunawa mata a lokutan tashe tashen hankula
2019-11-27 13:14:34        cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka dake aiki a kasar Somalia ko AMISOM a takaice, ta gudanar da wani dandali na wayar da kan al'umma game da bukatar kawo karshen muzgunawa mata a lokutan da ake fuskantar tashe tashen hankula. Yayin taron da ya gudana a birnin Mogadishu a jiya Talata, wanda AMISOM din ta shirya, an jaddada bukatar samar da kariya ga matan da suka taba fuskantar wannan matsala.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, jami'ar ofishin dake lura da samar da kariya ga mata ta AMISOM Gloria Jasse, ta ce a tsawon kwanaki 16 na wannan gangami, AMISOM za ta gudanar da tarukan karawa juna sani, da na wayar da kan jama'a a sassan kasar ta Somalia, da nufin kawo karshen cin zarafin mata, da kananan yara, wanda bangare ne na shirin wayar da kai da AMISOM din ke aiwatarwa tsakanin al'umma.

Dandalin dai ya hallara mahalarta daga kungiyoyin matasa, da na mata, da 'yan majalissun dokoki a matakin farko na al'umma, da wakilan al'ummun da rigingimu suka raba da muhallan su, da ma wakilan gwamnati, a wani yunkuri na zakulo ayyukan cin zarafi, da daukar matakan ba da tallafi ga hakan ya shafa a mataki na al'umma, da tsara manufofi, da ma daukar matakai na gaba, ga wadanda suke bukatar hakan.

An kebe ranar 25 ga watan Nuwambar ko wace shekara, domin kaddamar da gangamin kwanaki 16, na yaki da cin zarafin mata, wanda ke kammala a ranar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa, wato 10 ga watan Disamba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China