Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 10 sun mutu wasu 11 sun jikkata yayin da dakarun tsaron Somali suka yiwa maharan otel kawanya a Mogadishu
2019-12-11 15:54:36        cri
Hukumomin 'yan sandan Somali sun tabbatar da karuwar yawan hasarar rayuka da aka samu daga harin yammacin ranar Talata a wani otel dake Mogadishu, babban birnin kasar Somali, inda adadin wadanda suka mutun ya kai 10, kana wasu mutanen 11 kuma sun samu raunuka.

Zakia Hussein, mataimakiyar kwamishinan 'yan sandan Somali, ta ce jami'an tsaro sun kawo karshen kawanyar da suka yiwa sanannen otel din nan na SYL na tsawon sa'o'i 7, bayan da suka samu nasarar kashe dukkan maharan 5.

Zakia ta fada cikin wata sanarwa cewa, an kawo karshen harin, kuma jami'an tsaro sun kashe dukkan maharan su 5, ta kara da cewa, sojoji biyu da fararen hula 3 sun rasa rayukansu a sanadiyyar harin.

A cewarta, sojoji biyu da fararen hula 9 sun samu raunuka a lokacin harin na otel, inda maharan suka yi amfani da manyan makamai a kusa da fadar shugaban kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China