Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta ce har yanzu cutar Ebola a Congo Kinshasa matsala ce dake bukatar daukin kasa da kasa
2019-10-19 16:45:18        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce har yanzu cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, matsalar lafiya ce dake bukatar daukin gaggawa daga kasa da kasa, duk da cewa adadin masu kamuwa da ita na ci gaba da raguwa cikin makonnin da suka gabata.

WHO ta cimma wannan matsaya ne bayan kammala taro na 5, na kwamitin bada agajin gaggawa da aka kafa karkashin dokokin takaita yaduwar cutuka na kasa da kasa na 2005, wanda Darakta Janar na WHO, Tedros Adhanom ya kira a jiya Juma'a.

Alkaluma na baya-bayan nan da WHO ta fitar, sun nuna cewa jimilar mutane 3,228 ne aka samu rahoton sun kamu da cutar a kasar, wadanda suka hada da 3,114 da aka tabbatar sun kamu da kuma 114 da ake tababa ko sun kamu.

A makonnin baya-bayan nan, adadin masu kamauwa da cutar na raguwa. Sai dai cutar ta daina barkewa a birane, inda ta koma yankunan kauyukan da ba a iya zuwa cikin sauki, inda ake ganin akwai yuwar cutar ta kara bazuwa a sabbin wurare, idan aka dakatar da ayyukan yaki da ita. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China