Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bayyana cutar numfashi a matsayin wanda ke bukatar daukin gaggawa
2020-01-31 16:02:01        cri
Darakta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce barkewar cutar numfashi ta coronavirus ta zama babbar barazana ga lafiyar al'umma wadda ke bukatar daukin gaggawa daga kasa da kasa.

Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai bayan wani taron sirri da kwamitin daukin gaggawa na hukumar ya yi, ya jaddada cewa WHO ba ta goyon bayan sanya takunkumin hana tafiye-tafiye ko na cinikayya kan kasar Sin.

Karkashin ka'idojin kiwon lafiya na duniya, darakta janar na WHO na da ikon ayyana barkewar cuta a matsayin mai barazana ga lafiyar al'umma, idan cutar ta cimma wasu sharruda da aka kayyade. Matakin na da nufin kara tattara duk wasu abubuwan da ake bukata daga kasa da kasa don dakile annobar.

Tun bayan fara aiki da ka'idojin a shekarar 2007, WHO ta ayyana wannan mataki kan cututtuka sau da dama.

Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da kansa ke jagorantar ayyukan aiwatar matakan kariya da na dakile cutar.

Ya kara da cewa, yadda Sin ta yi saurin gano barkewar cutar, da nazarinta tare kuma da bayyanata ga WHO da kuma duniya, da kuma kudurin kasar na tsare gaskiya da taimakawa sauran kasashe, ya cancanci yabo. Yana mai cewa, kasar Sin ta bullo da wani sabon tsarin tunkarar barkewar cuta daga bangarori da dama.

Ya ce wannan ba yadda kasar Sin ta himmantu wajen kare rayuka da lafiyar jama'arta kadai yake nunawa ba, har ma da irin kokarinta na karewa da takaita yaduwar cututtuka a duniya.

Ghebreyesus, ya ce ya yi ammana kasar Sin za ta dakile tare da cin galaba kan cutar, yana mai cewa, kokarin Sin na yaki da cutar na bukatar yabo da girmamawa, hakazalika, abun koyi ne. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China