Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yi kira da a samar da wani dandali na gama gari da zai inganta kiwon lafiya
2019-11-11 10:50:19        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi kira da a samar da dandalin da dukkan al'umma za su iya shiga a dama da su, domin gaggauta samun nasarar muradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa a bangaren lafiya.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, Darakta Janar na WHO, ya shaidawa wani taron kiwon lafiya a Nairobi cewa, idan kasashen duniya na son hidimomin kiwon lafiya su isa ko ina, to dole ne a ba bukatun wadanda da aka bari a baya muhimmanci, ciki har da mata da yara da matasa.

Ya ce WHO na kira ga kowacce kasa, ta kafa wani dandali da zai kunshi kowa da kowa, wanda zai hada mutane daga dukkan fannonin kungiyoyin al'umma da bangarori masu zaman kansu da malamai da iyayae da mutane masu rauni kamar mata matalauta da yara, don su tattauna da mambobin majalisun dokoki da kuma gwamnatoci .

Darakta Janar din ya bayyana haka ne yayin bude taro na 24 kan hadin gwiwa a fannin lafiyar mata masu juna biyu da jarirai da kuma yara.

Manufar taron ita ce, musayar shaidun dake nuna ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiyar mata da yara da matasa, ta fuskar cimma tsarin kiwon lafiya na gama gari da kuma muradun ci gaba masu dorewa. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China