Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Nasarorin yaki da cutar AIDS sun fara raguwa saboda rashin maida hankali
2019-12-03 11:01:37        cri
Tedros Adhanom Ghebreyesus, darakta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya bayyana cewa nasarorin da ake samu a yaki da cuta mai karya garkuwar jiki AIDS sun fara ja da baya saboda da sakaci wajen daukar kwararan matakan siyasa da karancin samar da kudaden gudanarwa.

A jawabinsa lokacin taron karawa juna sani na kasa da kasa kan yaki da cutar AIDS, babban jami'in hukumar WHO ya ce, a shekarar 2018, mutane 770,000 sun mutu a sanadiyyar kwayoyin cutar HIV sannan an samu sabbin mutane miliyan 1.7 da suka kamu da kwayoyin cutar da kuma hasarar rayuka masu yawa sanadiyyar cutar kuma galibin matsalar tafi kamari a nahiyar Afrika.

Ya bayyana a jawabin bude taron kasa da kasa kan yaki da cutar AIDS da sauran cutukan da ake dauka ta hanyar jima'i a Afrika (ICASA), a Kigali tsakanin 2-7 ga watan Disamba ya ce, za'a samu nasarar shirin yaki da cutar a duniya ne idan aka yi amfani da fasahohin zamani, da shigar da dukkan al'ummar yankunan duniya cikin shirin, da kuma daukar matakai daga shugabannin siyasa.

Shugaban taron na ICASA, John Idoko, ya ce, cutar mai karya garkuwar jiki wato HIV za ta ci gaba da zama babbar barazana ga kasashen duniya a nan gaba.

Ya bukaci gwamnatocin kasashen duniya su dauki karin matakai na cikin gidan kasashensu wajen kawar da cutar ta HIV/AIDS baki daya daga Afrika.

Taken traon shi ne, "Kawar da cutar AIDS daga Afrika" taron ya samu halartar wakilai 8,000 da suka hada da shugabanni, kungiyoyin fafutuka, kwararrun masana kimiyya, da masu nazari, daga sassa daban daban na duniya domin tattaunawa game da rawar da shugabannin siyasa za su taka, tare da hadin gwiwar fasahohin zamani don kawo karshen cutar AIDS nan da shekarara 2030. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China