Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hangen Dala ba shi ne shiga birni ba
2020-02-04 20:24:19        cri
A 'yan kwanakin da suka gabata, kasar Sin ta dauki matakan da suka dace wajen ganin bayan cutar numfashin da ta bullo a kasar. Haka kuma kasashen duniya sun bayyana kudirinsu na baiwa kasar Sin goyon baya da ma taimakon da ya dace ta fannoni daban-daban, ta yadda za ta yaki wannan annoba. Sai dai kuma, a baya-bayan nan sakataren cinikayya na Amurka Wilbur Ross ya wallafa wani labarin karya cewa, annobar cutar da ta barke a kasar ta Sin ta taimakawa bangaren masana'antun samar da kayayyaki komawa kasar Amurka. Kalamansa ya gamu da tofin Allah tsine daga al'ummomin kasa da kasa.

Sharhin da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya wallafa a yau, ya yi nuni da cewa, annobar da ta barke, kalubale ne dake shafar bil-Adama baki daya, kuma ba batu na wata kasa ita kadai ba. A halin yanzu, gwamnatin kasar Sin ta bullo da managartan matakai masu tsauri na kandagarki da ma hada yaduwar wannan cuta, galibinsu sun ma zarce ka'idoji na lafiyar kasa da kasa. Kasar Sin ta dauki wadannan matakai ne ba don ta kare al'ummominta kadai ba, har ma da dukkan al'ummar duniya.

Sai dai kuma, kasar dake daukar kanta a matsayin babbar kasa a duniya, wato Amurka, har maganar da ake yanzu, ba ta baiwa kasar Sin ko da wani taimako ba. Baya ga haka, ta hana Sinawa shiga kasarta, matakin da ya haifar da zaman dar-dar.

Kalaman da sakataren cinikayyar Amurka ya furta, na yin amfani da batun annobar Corona, rashin tausayi ne kuma ya saba hankali, ya kuma kara nuna tsantsan son kai na wasu 'yan siyasar Amurka, da ma makircin dake cikin zukatansu. Ya kuma kara nuna imanin da Amurka ke da shi cewa, annobar da ta bullo a kasar Sin, tamkar karin maganar malam Bahaushe ne wai "gaba ta kai su gobarar Titi"

Haka kuma, sakatare Wilbur Ross, bai san komai game da batun tattalin arziki ba, kuma ai, ganin Dala, ba shi ne shiga birni ba. Bai fahimci cewa, hada karfi da karfe a tsakanin kasa da kasa dangane da fifikon tattalin arzikin kasashe, zai taimaka ga cin moriyar juna ba, da ma an ce hannu daya ba ya daukar jinka.

A bisa ga matakan da gwamnatin Amurka ke dauka kan farfado da masana'antun kasar, Wilbur Ross yana fatan yin amfani da annobar da ta bulla a kasar Sin wajen dawo da masana'antun samar da kayayyaki zuwa Amurka. Masu iya magana na cewa, na gaba ya yi gaba, na baya sai tsinkaye. Wanda ya riga ka barci, ai dole ya riga ka tashi.

Kasar Sin dai tana da yawan al'ummar da ta kai biliyan 1.4, da karuwar al'umma masu tsakaicin wadata, da daruruwan miliyoyin kawarraun 'yan kwadago, kayayyakin sadarwa na zamani, kana kasar da ke kan gaba a fannin samar da kayayyaki a duniya.

Kasar Sin tana da manyan kamfanoni da ke samar da kayayyakin da ake bukata, wanda kuma yana da muhimmanci ga alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Babu tantanta annobar da ta bullo a halin yanzu, za ta shafi tattalin arzikin kasar Sin. Ai dama ba kullum ake kwana a gado ba, amma hakan na dan wani lokaci ne. Kasuwannin kasar Sin za su iya jure wannan tasiri, kana yanayin ci gaban tattalin arzikin kasar ba zai yi wani canja ba. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China