Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta nuna fifikonta na dalike cutar numfashin da ta bulla a kasar
2020-01-29 22:04:09        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a jiya Talata ya gana da babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a nan birnin Beijing, inda ya jaddada cewa, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma bisa fifikon tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin, da dogaro da jama'a, da niyya, hada kai da taimakawa juna, yin rigakafi da shawo kan cuta ta hanyar kimiyya, daukar matakai masu dacewa, muna cike da imani da karfi na cimma nasarar yaki da cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa da ta bulla a kasar. Game da haka, Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, a yayin da kasar Sin ke tinkarar yanayin annobar cutar, ta dauki managartan matakai cikin sauri, wadanda ba a taba ganin irinsu ba a duniya, hukumarsa ta yaba sosai da wannan.

 

 

Bayan da cutar numfashin ta bulla a kasar Sin, kasar ta shafe mako guda da wani abu don tabbatar da abun da ya haddasa cutar, matakin da ya karya bajintar duniya a wannan fannin. Ban da wannan kuma, ta rufe hanyoyin shiga da fita daga birnin Wuhan na dan lokaci, da tsaida kudurin kafa asibitocin wucin gadi guda biyu a birnin. A ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin na ba da muhimmanci ga batutuwan da suka shafi tsaron al'umma, gami da lafiyarsu, 'yan kasar kuma sun yi duk mai yiwuwa, wajen tabbatar da dakile yaduwar cutar. Akwai larduna da jihohi guda 30 na kasar Sin da suka kaddamar da matakan da suka kasance matsayin koli don tinkarar cuta mai tsanani da ta bulla ba zato ba tsamani, wanda ya shafi mutane sama da biliyan 1.3. Wadannan matakan da aka dauka sun nuna kwarewar kasar Sin na karfafa al'umma gwiwa, da karfinta na gudanar da harkokin kasa, da kwarewarta wajen dalike da shawo kan cutar.

 

 

Har yanzu dai ana fuskantar yanayi mai tsanani na yaki da cutar, Sinawa na kokari ne ba domin kiyaye rayuwarsu kawai ba, har ma da lafiyar jama'ar duniya baki daya. Bisa ingancin tsarin kasar, da tabbacin da aka samu a fannin kimiyya da fasaha, kasar na cike da Imani da karfi na ganin bayan cutar cikin nasara. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China