Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda take yin rigakafi da shawo kan cutar numfashi jarrabawa ce da aka yi wa kasar Sin
2020-01-27 17:39:09        cri

Yau Litinin, rana ta uku ce ta sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, yanzu dai Sinawa na fama da cutar numfashi da kwayoyin cutar coronavirus ke haifarwa. A yayin da ake kuma fama da zirga-zirgar fasinjoji a yayin bikin bazara, wanda ake kiransa "Kaurar dan Adam mafi girma a kasa", aikin ja wur da kuma gaggawa ne a tinkari wannan cuta.

 

Ko shakka babu wannan cutar numfashi da ta bulla a birnin Wuhan na kasar Sin, ta kasance wata sabuwar jarrabawa ga kasar Sin mai yawan al'umma sama da biliyan 1.4 kan kwarewarta ta gudanar da harkokin kasar. A yayin da ake fuskantar saurin yaduwar cutar, aka gano cewa, kasar Sin tana ta daukar matakai a jere: kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS ya kafa kungiyar bada jagoranci don tinkarar yanayin annobar cutar, majalisar gudanarwar kasar Sin ta sanar da tsawaita lokacin hutu na bikin bazara, hukumar lafiyar kasar tana sanar da yanayin da ake ciki kan yaki da cutar a kowace rana, ana ta turo masu aikin jinya da na'urori da kayayyaki zuwa lardin Hubei, da gina asibitin wucin gadi cikin gaggawa a birnin Wuhan da dai sauransu. Lallai kasar Sin ba ta bata lokaci ko kadan ba daga tsaida kuduri har zuwa zartas da su, hakan ya shaida yadda kasar ke yin iyakar kokarinta wajen kiyaye tsaron jama'a da kiwon lafiyarsu.

 

Abun da ya cancanci a lura da shi shi ne, gudanar da ayyukan yin rigakafi da shawo kan cutar bisa doka, ya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar. Yanzu dai, akwai larduna da jihohi guda 30 na kasar Sin da suka kaddamar da matakan da suka kai matsayin koli da nufin tinkarar cutar mai tsanani da ta bulla ba zato ba tsamani.

A waje guda kuma, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa kan sanar da yanayin yin rigakafi da shawo kan cutar da ake ciki a bayyane cikin lokaci, kana kasar Sin tana raba fasahohin da ta samu wajen yaki da cutar tare da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, game da haka, babban daraktan hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin, a ganinsa, wannan ya nuna rawar da mahukuntan kasar Sin ke takawa a fannin kiwon lafiyar duniya baki daya.

Game da jerin matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar numfashin, mujallar The Lancet wadda ta shahara a fannin likitanci a duniya ta ba da sharhi cewa, kebe wadanda ba a kai ga tabbatar da ko sun kamu da cutar ba tukuna, da wadanda suka yi cudanya ta kusa da masu dauke da cutar, wasu dabaru ne na ganowa da magance cutar, da wayar da kan jama'a a fannin, da dai sauransu, dukkansu sun nuna cewa, matakan da kasar Sin ta dauka na yaki da cutar numfashin sun kusa kaiwa ga ma'aunin kasa da kasa. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China