2020-01-23 21:24:14 cri |
Wannan ba shi ne karon farko da kasashe daban-daban suke daukar irin wannan mataki na kandagarki ba domin shawo kan yaduwar cututtuka a tarihin dan Adam. Alal misali, a shekara ta 2014, domin hana yaduwar cutar Ebola, wasu kasashen Afirka ciki har da Guinea da Saliyo da kuma Laberiya sun sanar da kafa wani kebabben wuri dake bakin iyakokinsu. Haka kuma babban darektan kungiyar lafiya ta duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna cewa, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka na da karfin gaske, kuma a ganinsa, yana da muhimmanci matuka da gwamnatin kasar Sin ta dauka irin wadannan matakan da suka dace da hakikanin halin da ake ciki.
Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan kandagarkin yaduwar cutar numfashi ba tare da bata lokaci ba kuma ba tare da wata rufa-rufa ba, al'amarin da ya nuna cewa kasar na daukar babban nauyin dake wuyanta ga duk duniya. Bayan da kungiyar WHO ta tura kwararrunta zuwa Wuhan don ganewa idanunsu halin da ake ciki, Mista Tedros Ghebreyesus ya ce, kasar ta Sin tana bayyana duk wani abun da ya shafi cutar numfashi gami da daukar matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar, gaskiya ba ta boye kome ba.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China