Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO Ta Fidda Sabuwar Manufa Ba Domin Nuna Rashin Amincewa Kan Kasar Sin Ba
2020-01-31 20:16:51        cri

Jiya Alhamis, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya sanar da ayyana cutar numfashi da ta bulla a kasar Sin a matsayin "harkar kiwon lafiya ta gaggawa dake janyo hankulan kasa da kasa". Kuma ya jaddada cewa, matakin da WHO ta dauka ba domin nuna rashin imani kan kasar Sin ba ne, ya ce, hukumar WHO tana da imani kan matakan da kasar Sin ta ke dauka wajen hana yaduwar cutar. Ban da haka kuma, WHO ba ta goyon bayan sanya takunkumin hana tafiye-tafiye ko na cinikayya kan kasar Sin.

A halin yanzu, cutar numfashi tana yaduwa da sauri, wannan sabon matakin da WHO ta dauka zai taimakawa kasashen duniya fuskantar yaduwar cutar, da kuma samar wa kasashen da ba su da isassun kayayyakin kiwon lafiya taimakon da suke bukata, ta yadda za a magance yaduwar cutar a tsakanin kasashen duniya.

Haka kuma, Ghebreyesus ya ba da shawarwari guda bakwai, da suka hada da cewa, babu bukatar sanya takunkumin hana tafiye-tafiye ko na cinikayya kan kasar Sin, da nuna goyon baya ga kasashen da ba su da isassun kayayyakin kiwon lafiya da kuma gaggauta nazari samar da allurar rigakafi da dai sauransu. Tedros Ghebreyesus ya bayyana haka ne bisa amincewarsa kan ayyukan da kasar Sin ta yi wajen hana yaduwar cutar, lamarin da zai sassauta damuwar da kasashen dunuya ke yi kan wannan cuta, da kuma magance daukar matakan da ba su dace ba kan kasar Sin, wadanda za su iya haddasa illa ga bunkasuwar tattalin arziki da cinikin kasa da kasa.

A halin yanzu, harkar kiwon lafiya ba ta da iyaka, ya kamata kasashen duniya su hada kansu domin hana yaduwar cutar numfashin da ta bulla. Kasar Sin ita ma za ta dauki dukkan matakan da suka dace ba tare da boye kome ba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da hukumar WHO, domin cimma nasarar yaki da cutar, da kuma kiyaye al'ummarta da ma al'ummomin duniya baki daya. (Mai Fassarawa: Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China