Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana da imanin cimma nasarar yaki da cutar numfashi
2020-02-04 12:16:13        cri

Zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS ya gudanar da taron tattaunawa kan yaki da cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa, inda aka yi nuni da cewa, wannan babbar jarrabawa ce da ta shafi tsarin gudanarwar harkokin kasar Sin, da ma karfin kasar. Taron ya yarda da cewa, aikin dake gaban komai shi ne yin namijin kokarin ba da jinya ga masu cutar, da tabbatar da samar da kayayyakin jinya, da rage yawan mutanen da suka kamu da cutar, da wadanda suka mutu a sakamakon harbuwa da cutar. Kana ana bukatar tabbatar da samar da abinci, da sauran kayayyakin zaman yau da kullum ya jama'a.

Ingancin tsari shi ne fifikon da wata kasa ke da shi. Don cimma nasarar yaki da cutar, ya kamata a bi jagorancin JKS, da tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, da dogaro ga jama'ar kasar, da karfafa imani da kuma hada karfi da karfe, don kandagarki da yaki da cutar. Don haka, an samu babban ci gaba kan batun tabbatar da kayayyakin jinya da na zaman yau da kullum.

Babu shakka, ingancin tsari na kasar Sin na zama karfin kasar na gudanar da harkokinta, da warware matsaloli, don sa kaimin samun galabar kandagarki da yaki da cutar.

A cikin shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, an kafa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin da tsarin gudanar da harkokin kasar, wadanda suka shaida ingancinsu a fannoni daban daban. A halin yanzu, ana fuskantar yanayi mai tsanani na kandagarki da yaki da cutar, wanda ke bukatar a daidaita matsaloli cikin sauri. A gun taron da aka gudanar a jiya, an yi nuni da cewa, ya kamata a koyi fasahohi da kyautata tsarin tinkarar al'amura na ba zata bisa matsalolin da aka gano, yayin da ake yaki da cutar a wannan karo. A kara sa ido kan yanayin kiwon lafiya na al'ummar kasar, da harkokin kasuwanci, da kara raya tsarin dokokin kasar, da kyautata tsarin adana kayayyakin kasar, da kuma inganta karfin samar da kayayyaki mafi muhimmanci a kasar.

An yi nuni da cewa, Sin tana daukar matakai bisa matsalolin da ake fuskanta yayin da ake magancewa, da yaki da cutar. Koda yake aikin na da matukar wuya, amma duk da haka an yi amfani da ingancin tsarin kasar, da dogaro da jama'ar kasar. Sin tana da imanin za ta cimma nasarar yaki da wannan cuta ta numfashi, da tabbatar da tsaro da lafiyar jama'ar kasar, da kuma inganta tsarin gudanar da harkokin kasar da karfinta. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China