Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta jingine zargin da ta yiwa Sin na rage darajar kudin kasarta
2020-01-14 11:04:00        cri

Kasar Amurka ta dakatar da zargin da ta yiwa kasar Sin cikin wani rahoto da sashen baitul-malin kasar ya fitar jiya Litinin, game da rage darajar kudin kasarta.

A cikin wani rahoton rabin shekara da ya fitar kan manufofin tattalin arziki da na musayar kudaden ketare kan manyan abokan huldar cinikayyar Amurka, sashen baitul-malin na Amurka ya bayyana cewa, a wannan lokaci dukkan manyan abokan huldar cinikayyarta ba su cika ka'idojin rage darajar kudadensu ba.

A nasa bangare sakataren baitul-malin Amurka Steven Mnuchin, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, kasar Sin ta bayyana kudirin kaucewa rage darajar kudinta, yayin da take yayata yin adalci da yin komai a bayyane. Yana mai cewa, sashen ya kimanta ci gaban da aka samu cikin watanni da dama da suka gabata kan yadda kasar ta Sin take aiwatar da manufofinta na kudi.

Shugaban dandalin hukumomi da harkokin kudi na kasar Amurka kana wakilin Amurka a asusun IMF, Mark Sobel ya bayyana a shafinsa na Twitteer cewa, wannan labari ne mai kyau, yana mai kiran zargin a matsayin surutun banza, abin da bai dace ba kuma batu na siyasa.

Sobel wanda har ila, ya taba zama mataimakin sakatare a sashen baitul-malin na Amurka ya ce, bai kamata a fara zargin kasar Sin da wannan batu ba.

A watan Agustan shekarar da ta gabata, yayin da ake tsaka da tankiyar cinikayya tsakanin Sin da Amurka, sashen baitui-malin Amurka ya yanke shawarar ayyana kasar Sin a matsayin mai rage darajar kudin kasarta, lamarin da ya janyo suka daga ciki da wajen kasar, inda aka kira matakin a matsayin maras tushe da ma abin da bai dace ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China