Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron kasa da kasa kan yawan al'umma a Kenya
2019-11-13 10:45:38        cri

An kaddamar da taron kasa da kasa kan yawan al'umma da samun ci gaba a birnin Nairobin Kenya, inda aka yi kira ga gwamnatoci da hukumomin kasa da kasa su inganta samar da magungunan kayyade haihuwa irin na zamani ga matan dake cikin shekarunsu na haihuwa.

Dubban wakilai da suka hada da shugabanni da ministoci da shugabannin hukumomin kasa da kasa da masu gangami da masu bincike ne suka halarci taron da ake sa ran zai farfado da ajandar duniya na takaita haihuwa.

A jawabinsa na bude taron, shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya ce mayar da hankali ga lafiyar mata da 'yan mata na da muhimmanci wajen rage mace macesu yayin haihuwa da kuma samun ci gaba mai dorewa.

Uhuru Kenyatta wanda ya ce kayyade haihuwa zai yi kyakkyawan tasiri kan bambancin jinsi da rage fatara, ya kara da cewa, kare hakkokin mata da zabinsu da kuma kyautatuwar rayuwarsu, shi ne hanyar samar da ci gaban al'umma.

Kenya da hadin gwiwar asusun kula da yawan al'umma na gwamnatin kasar Denmark ne suka karbi bakuncin taron da zai gudana har zuwa gobe 14 ga wata, da nufin kara karfin kudurin shugabanci da fitar da kudi, wajen tabbatar da matan dake cikin shekarunsu na haihuwa sun samun magugunan kayyade haihuwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China