Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin raya harkokin cinikayya na nahiyar Afrika zai zuba dala miliyan 500 ga sana'ar kirkire kirkire da al'adu
2020-01-18 17:19:34        cri
Bankin raya harkokin cinikayya na nahiyar Afrika, zai zuba dala miliyan 500 domin tallafawa sana'ar kirkire kirkire da al'adu na nahiyar, cikin shekaru 2 masu zuwa.

Bankin ya sanar da matakin nasa ne yayin bude wani taron musaya na Afrika na yini 2 da kamfanin Times Multimedia da bankin da Gwamnatin Rwanda suka shirya.

Shugaban Bankin Benedict Oramah, ya ce sana'o'in kirkire-kirkire na da karfin samar da manufofin ci gaba mai dorewa na bai daya ga kasashen Afrika.

Ya ce Afrika na rashin kayayyakin more rayuwa da karfin tallata basirarta ta kirkire kirkire tare da cin moriyar dake tattare da ita.

Kudaden, wanda kari ne akan abun da yanzu haka bankin ke aiwatarwa, za a iya samunsu ne ta hanyar karbar rancen bankuna da samar da kudi kai tsaye ga masu sana'o'i.

Har ila yau, ya ce bangaren na bada gagagrumar gudunmuwa ga samar da kayayyaki a cikin kasashen nahiyar, sannan yana ingiza ci gaban tattalin arziki ta hanyar hadawa da tafiya da dukkan al'ummomi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China