Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin kasashe daban-daban na da imanin ganin Sin ta cimma nasarar yaki da cutar numfashi
2020-02-03 11:12:27        cri
Kokarin yaki da cutar numfashi da Sin take yi na jawo hankalin kasa da kasa, a kwanakin baya-baya nan, shugabannin kasa da kasa na jinjinawa matakai masu dacewa da Sin take dauka don yaki da cutar, suna mata goyon baya tare da imanin cewa, Sin za ta cimma nasarar wannan yaki.

Shugaban jam'iyyar Jubilee mai mulki a kasar Kenya Raphael Tuju, ya shaidawa manema labaran kasar Sin cewa, Sin ta dauki matakai da suka dace masu inganci don yaki da cutar, wanda hakan abun jinjinawa ne matuka. Ban da wannan kuma, yana matukar darajanta kwarin gwiwar da jama'ar kasar Sin ke bayyanawa a wannan muhimmin lokaci. Ya ce, yana da imanin cewa, Sin za ta dakile wannan cuta, yana kuma marawa birnin Wuhan har ma kasar Sin baki daya baya.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Georgia David Zalkaliani, ya wallafa sako a shafin sa na Twitter dake cewa, yana tare da kasar Sin a wannan mawuyancin hali, na fama da cutar numfashi, kuma kasashen biyu za su kara hadin kansu wajen dakile yaduwar cutar.

Shi kuwa mataimakin shugaban kwamitin ba da ilmi da kimiyya na majalisar wakilan kasar Rasha Gennady Onishchenko bayyanawa manema labarai ya yi cewa, yana jinjinawa matakan da Sin ke dauka na bude kofa, da adalci, da sauke nauyin dake wuyanta, kuma sakwannin da Sin ta bayar a fili na da amfani sosai wajen nazari da yaki da cutar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China